Labarai
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana marigayi Alhaji Aminu Dantata a matsayin mutum mai tausayin jama’a da jajircewa wajen ci gaban Najeriya.

Shugaban kasar ya bayana hakan ne a yau Jumaa a wata ziyarar ta’aziya daya kawo nan Jahar Kano ga iyalan marigayin.
Shugaban ya Kuma bayyana shi a matsayin mutum mai gaskiya, karamci da taimakon jama’a ta hanyoyi da dama.
Alhaji Aminu Dantata, ya rasu yana da shekaru 94, yana daga cikin manyan ’yan kasuwa kuma masu taimakon jama’a a Najeriya.




