Labarai

Matatar Dangote ta bayyana takaici a kan yadda wasu daga cikin abokan hulɗarta suka karya yarjejeniyar saukaka wa talakawa.

Binciken da matatar ta gudanar ya gano wasu daga cikin abokan hulɗar na karkatar da kayayyakin zuwa ga dillalan da ba su da rajista wadanda suke sayarwa jama’a da tsada.

Jaridar Punch ta wallafa cewa binciken ya gano yadda wasu masu dillanci da aka ba su fetur a farashi mai rangwame domin sauƙaƙa wa jama’a na sayar wa waɗansu yan kasuwa.

Matatar ta Dangote tace hakan ya karya tsarin da aka shimfiɗa domin tallafawa abokan kasuwancin da kuma tabbatar da wadatar fetur a faɗin ƙasarnan.

Dangote ya ce waɗannan dillalan na amfani da takardar rajistarsu don karɓar fetur daga matatar, amma sai su bai wa wasu masu shigo da kaya damar karɓa a madadin su.

Ya ce su kuma wadancan yan kasuwa suna sayar da shi a kasuwa a farashi mafi tsada, suna kauce wa caji na dakon mai da sauran tsarabe-tsaraben da ya hau kansu.

Wannan rufa-rufa da matatar Dangote ta gano ne `ya sa ta ɗauki matakin dakatar da tsarin sayar da man fetur a farashi mai rahusa ga abokan hulɗarsa.

Wannan batu dai na kunshe a cikin wata wasikar dakatarwar da aka tura ga abokan hulɗar matatar a ranar 13 ga Yuli 2025, wanda Daraktar Ayyuka na kasuwanci Fatima Dangote, ta sanyawa hannu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button