Labarai
A ci gaba da biyan hakkokin ma’aikatan da Suka bar aiki a JIhar kano gwamnan Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sake kaddamar da biyan Naira biliyan shida a Karo na hudu.
Da yake jawabi yayin kaddamar da biyan kudin a gidan gwamnati, gwamna Yusuf ya ce Yan fanshon da za, a biya a wannan Karon sun hada da maaikatan da suka ritaya tun daga shekara ta 2020 zuwa shekara ta 2023 ya na Mai cewa tuni gwamnatin ta sake ware wasu Naira biliyan biyar domin sake biyan wasu yan fanshon nan da watan Augusta mai zuwa.
Abba Kabir Yusuf ya Sha alwashin kammala biyan dukkanin basukan da Yan fanshon jihar ke bi kafin kammala wa’adin mulkinsa.
Gwamnan ya ce sun gaji basukan Yan fansho da yawansu ya Kai Naira biliyan 48 Wanda zuwa yanzu an biya naira biliyan 22.



