Labarai
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya buƙaci hukumomin tsaro da su inganta hanyoyin da suke bi wajen yaƙi da rashin tsaro a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan wasu ’yan bindiga sun kashe manoma 27 a ƙauyen Bindi, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom, a ranar Litinin.
Rahotanni sun ruwaito cewa gwamnan ya nuna damuwa matuƙa akan lamarin
Yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai ƙauyen a ranar Laraba, Gwamna Mutfwang ya ce: Abin baƙin ciki ne duk da cewa sun samu bayanan sirri game da harin amma duk da haka sai da aka kai harin.



