Labarai
Alhaji Aliko Dangote zai gina katafariyar tashar jiragen ruwa a Nigeria.

Attajiri mafi kudi a nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote ya fara neman lasisin gina tashar jiragen ruwa mafi girma kuma mafi zurfi a Nijeriya, a garin Olokola da ke jihar Ogun, kamar yadda rahoton Bloomberg ya bayyana.
Sabuwar tashar jirgin ruwa ta Atlantika za ta kasance mai matuƙar tasiri ga harkokin sufuri da fitar da kaya na kamfanin Dangote, musamman wajen tallafawa manyan masana’antunsa na takin zamani da sinadarai.
An shirya gina tashar ne kimanin kilomita 100 daga masana’antun Dangote da ke Lagos.




