Labarai

An maka Sarkin Kano a gaban kotu tare da wasu mutane 12.

Wasu tsoffin jami’an fadar Kano sun maka Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, da wasu mutane 12 gaban kotu, bisa zargin korar su daga matsugunansu a cikin fadar Kano tare da rusa gidajen kakanninsu da ke cikin harabar fadar.

Sun shigar da ƙarar ne a kotun ƙolin jihar Kano, sashin Bichi, ƙarƙashin jagorancin Usman Dako (Galadiman Sallama). Sauran waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Auwalu Maikudi (Sarkin Lema), Sani Mohammad (Sani Kwano), Abba Mohammad (Sarkin Tafarki), da wasu.

Waɗanda aka shigar da ƙara sun haɗa da Sarki Sanusi II, Majalisar Sarakunan Kano, da wasu masu muƙaman fada ciki har da Sarkin Yaƙin Kano, Shamakin Kano, Halifan Shamaki, da sauransu. Haka kuma, Rundunar Ƴansanda, da DSS, da NSCDC sun haɗu acikin waɗanda aka shigar da ƙara.

Lauyan masu ƙarar, Hassan Tanko Kyaure, ya buƙaci kotu da ta dakatar da korar su tare da bayar da kariya gare su, yana mai cewa hakan ya samo asali ne daga rikicin biyayya tsakanin mabiya Sarki Sanusi da na sarkin da aka tuɓe, Aminu Ado Bayero.

Kotun, ƙarƙashin mai shari’a Musa Ahmad, ta umarci ɓangarorin da su ci gaba da kasancewa a matsayin da suke kafin ƙarar, sannan ta amince da miƙa takardun kotu ga waɗanda ke Kano ta hanyar majalisar sarakuna, yayin da waɗanda ke wajen jihar za su karɓi takardunsu ta hanyar aika.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button