Labarai
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutane 98 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi, sata, zamba da kuma tayar da hankalin jama’a.

An kama waɗannan mutane ne ƙarƙashin sabon samamen da rundunar ta ƙaddamar mai suna “Operation Kukan Kura” wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli, 2025.
Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Alhamis.
Ya ce wannan aiki wani ɓangare ne na ƙoƙarin daƙile aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya a faɗin Jihar Kano.



