Labarai

Matatar man Dangote ta sake rage farashin man fetur zuwa Naira 820 kan kowace lita, daga Naira 840 da ake sayarwa a baya.

Mai magana da yawun matatar Dangote, Mista Anthony Chiejina, ya tabbatar da rage farashin a Legas inda yace wannan sabon farashi zai fara aiki nan take.

A makon da ya gabata, matatar ta rage farashin daga Naira 880 zuwa Naira 840 yanzu kuma ta ƙara ragewa zuwa Naira 820.

Yayin da matatar ke tabbatar da samun isasshen man fetur a ƙasa, ‘yan kasuwa sun nuna sha’awar siyan man daga matatar Dangote saboda ingancin man da kuma tabbacin wadatarsa.

Ya bayyana cewa rage farashin da aka yi a baya zuwa Naira 840 ya faru ne sakamakon hauhawar farashin ɗanyen mai a duniya sanadiyyar rikicin da ya auku a Gabas ta Tsakiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button