Malaman makarantun firamare da ke ƙarƙashin Hukumar Ilimin Ƙananan Hukumomi (LEA) a babban birnin tarayya Abuja sun janye yajin aikin da suka tsunduma watanni uku da suka gabata.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Maris ne dai malaman da ke ƙarƙashin ƙungiyar malamai ta ƙasa NUT suka tsunduma yajin aikin kan abin da suka kira rashin byan haƙƙoƙinsu na mafi ƙarancin albashi da aka ƙayyade na Naira dubu 70.
A ranar Alhamis din makon jiya ne Ministan Abuja, Nyesome Wike ya gana da shugabannin ƙungiyar malaman daga ƙananan hukomomi shida na Abuja da wasu masu ruwa da tsaki.
Bayan wannan ganawar ne gamayyar ƙungiyoyin malaman a yammacin ranarTalata ta sanar da janye yajin aikin wanda ta ce zai fara ne daga yau Laraba, 9 ga watan Yulin 2025.
Shugabannin ƙungiyoyin malaman da suka sanya hannu a takardar janye yajin aikin sun bayyana cimma wannan matsaya ce bayan sakin wani kaso da ya kai kusan naira biliyan 16 na bashin da za a biya malaman albashinsu na watannin da dokar sabon mafi ƙarancin albashin ta soma aiki.




