Labarai
’Yan sanda sun kama wani matashi mai shekaru 24 kan zargin ya kashe mahaifinsa mai shekaru 70 a ƙauyen Uzum da ke Ƙaramar Hukumar Giade ta jihar Bauchi.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce matashin ya yi amfani da sanda ne ya bugi mahaifin nasa a kai, nan take dattijon ya faɗi ya mutu.
Wani mazaunin ƙauyen Uzum da ke Giaɗe ya ce wanda ake zargin ya lakaɗa wa mahaifinsa duka ne da sanda yayin da suke taƙaddama a gida da misalin karfe 10:30 na daren ranar Alhamis din da ta gabata.
Wakil ya bayyana wa manema labarai a ranar Juma’a a Bauchi cewa a ranar Alhamis da dare ne wani mutumin kirki ya kira su a ranar ya sanar da su.
Ya ci gaba da cewa rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike, yayin da wanda ake zargin kuma yana hannun ’yan sanda kuma bayan an kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu.



