Labarai

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sunbude wuta a gidan wani tsohon minista 

Maharan sun kai hari gidan tsohon Ministan Wasanni na Tarayya, Damishi Sango, da ke ƙauyen Dalwal a ƙaramar hukumar Riyom ta Jihar Filato, inda suka hallaka wata mata tare da jikkata jami’in ɗan sanda.

Wata majiya daga yankin ta tabbatar da cewa an harbe wata mace har lahira, wacce rahotanni ke cewa ƴar uwa ce ga tsohon ministan. Hakazalika, wani jami’in ƴan sanda mai suna Sifeta Walba Go Tom daga SPU Base 4, Makurdi, ya samu raunuka a yayin da ya yi ƙoƙarin mayar da martani.

Bayan harbin, maharan sun kwace bindigar jami’in ƴan sandan kafin su tsere ba tare da an cimma su ba.

Wasu mazauna yankin sun ce har zuwa lokacin da jami’an tsaro suka iso wajen, maharan sun riga sun ɓace da gabar su.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa tuni an fara bincike domin kamo wadanda suka aikata wannan ta’asa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button