
Shugaban hukumar NAFDAC na Jihar Bauchi, Hamis Yahaya, ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Bauchi, ranar Talata.
Hydroquinone sinadari ne da ake amfani da shi wajen rage duhun fata ko tabo.
A cewar Yahaya, hukumar ta NAFDAC ta amince da kaso biyu kacal (2%) na hydroquinone a cikin kayan kwalliya don kiyaye lafiyar masu amfani da irin wadannan mayukan.
Ya bayyana cewa NAFDAC na gudanar da bincike a kasuwanni don tabbatar da cewa kayayyakin da ake amfani da su ba sa cutar da lafiyar jama’a.
“Fatar mutum mai duhu tana da kariya daga hasken rana saboda sinadarin melanin da ke cikinta. Amfani da man da ke dauke da hydroquinone fiye da kashi biyu cikin dari (2%) yana da illa ga lafiya. Haka kuma, hada man shafe-shafe ba tare da kwarewa ba babban kuskure ne. Hydroquinone na iya haifar da cututtuka daban-daban da suka hada da ciwon daji (cancer),” in ji shi.



