Malaman wasu makarantu a Jihar Kano na samun sabbin horo kan yadda zasu tallafawa ɗalibai ta fuskar tunani da tarbiyya, domin kare su daga fadawa cikin miyagun dabi’u da laifukan da ke ƙaruwa a tsakanin matasa.

Malaman wasu makarantu a Jihar Kano na samun sabbin horo kan yadda zasu tallafawa ɗalibai ta fuskar tunani da tarbiyya, domin kare su daga fadawa cikin miyagun dabi’u da laifukan da ke ƙaruwa a tsakanin matasa.
Wata kungiyar rajin kawo sauyi da wayar da kai a cikin al’umma ce ta shirya taron a ƙarshen mako, wanda ya haɗa malamai daga makarantu sakandare guda 100.
Taron ya mayar da hankali ne kan rawar da malamai zasu iya takawa wajen kare matasa daga gurɓatattun al’amura, ta hanyar jawo su a jiki da kuma fahimtar matsalolinsu.
A wajen taron, Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, Alhaji Nasiru Sule Garo, wanda Hajiya Samira Umar Adamu ta wakilta, ya jaddada cewa malamai su ne ginshiƙan kafa kyakkyawar makoma ga ɗalibai.
Ta bayyana cewa kusanci da dalibai da basu shawara na taimaka wajen dakile hulɗarsu da abokan da ke da tasiri mara kyau.
A nasa jawabin shugaban ƙungiyar Humanity Development for Change, Comrade Adamu Balarabe, yace taron na daga cikin shirye-shiryen haɗin gwiwa da gwamnatin jiha domin farfaɗo da sashen bada shawarwari da jagoranci ga ɗalibai a makarantu, wanda zai taimaka wajen rage yawan shaye-shaye da rikice-rikicen daba da ke addabar matasa.




