Ketare

Isra’ila ta kashe sama da mutane 300 a Gaza cikin sa’o’i 48 yayin da tsagaita wuta ke cikin hali na rashin tabbas

Fiye da Falasdinawa 300 ne sojojin Isra’ila suka kashe a cikin awanni 48 da suka gabata, a cewar Ofishin Watsa Labarai na Gwamnatin Gaza, wanda ya ce Isra’ila ta “aikata kisan kiyashi guda 26 a cikin wannan lokaci.

Akalla mutane 73 ne Isra’ila ta kashe tun daga wayewar gari a ranar Alhamis, ciki har da mutane 33 masu neman taimako a cibiyar taimakon Gaza Humanitarian Foundation (GHF) da Isra’ila da Amurka ke goyon baya.

Mutane goma sha uku sun mutu lokacin da sojojin Isra’ila suka kai hari kan wani tantin a al-Mawasi a kudu, yayin da mutane 11 suka mutu kuma da dama suka ji rauni a wani hari kan Makarantar Mustafa Hafez, inda aka tsugunar da mutanen da suka rasa matsuguni a yammacin birnin Gaza, majiyoyin lafiya sun shaida wa Al Jazeera.

Sanarwar Ofishin Yaɗa Labarai na Gwamnati a ranar Alhamis ta ce hare-haren da aka kai cikin awanni 48 da suka gabata sun yi akan fararen hula ne dake neman mafaka a cibiyoyin ‘yan gudun hijira da ke cike da dubban mutane da suka rasa matsuguni, wuraren hutun jama’a, iyalan Falasdinawa a cikin gidajensu, kasuwannin da muhimman wuraren fararen hula, da kuma fararen hula masu fama da yunwa suna neman abinci.

Fiye da ƙungiyoyin jinƙai 130, ciki har da Oxfam, Save the Children da Amnesty International, a ranar Talata sun nemi a rufe GHF nan take, suna zarginsu da taimakawa hare-hare kan Falasdinawa masu yunwa.

Tun lokacin da GHF ta fara aiki a ƙarshen Watan Mayu, fiye da Falasɗinawa 600 sun mutu yayin neman taimako, kuma kusan 4,000 sun ji raunuka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button