Labarai
Gwamnatin Jihar Yobe ta sanar da rufe wasu kasuwanni uku na mako-mako na ɗan wani lokaci, saboda tsoron yiwuwar hare-haren Boko Haram.

Kasuwannin da abin ya shafa su ne na Katarko, Kukareta da Buni Yadi, dukkaninsu a Ƙaramar Hukumar Gujba.
An rufe su ne domin taimakawa aikin da jami’an tsaro ke yi wajen yaƙar ’yan ta’adda a faɗin jihar.
A cewar Mai Bai Wai Gwamnan Yobe Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya), an rufe kasuwannin ne don bai wa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukansu cikin sauƙi tare da inganta tsaro a yankunan da abin ya shafa.



