Labarai
A bayan sallar Laasar ne a yau Talata ake sa ran za a gudanar da jana’izar fitaccen attajirin nan Alhaji Aminu Ɗantata a masallacin Madina.
Mataimakin marigayin na musaman Mustapha Junaid ya shaida wa BBC cewa shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana’izar.
A ranar Asabar ne shahararren ɗankasuwa Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a hadadiyar daular Larabawa.



