Labarai
’Yan sanda sun fara neman wani mutum mai shekara 55, wanda ake zargin ya yi wa matarsa kisan gilla da adda a garin Babbangida da ke Karamar Hukumar Tarmuwa ta Jihar Yobe.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Dungus Abdulkarim, a cikin wata sanarwa ya ce wanda wanda ake zargin ya yi wannan aika-aika ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a, 28 ga watan Yuni a kauyen Koriyel.
Tuni dai ’yan sanda suka fara kokarin cafke wanda ake zargin dan ya fuskanci shari’a.
A wani labarin kuma, ’yan sanda sun kama wasu mutane biyu da kasa zargin sun kashe wani mutum bisa zargin satar waya a garin Ngalda da ke Ƙaramar Hukumar Fika.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar Yobe, Emmanuel Ado, ya bukaci mazauna yankin da su nemi hanyoyin warware rigingimu cikin lumana, su guji daukar doka a hannunsu.




