Ketare

Shugaban adawa na Tanzaniya zai kare kansa a kotu kan tuhumar cin amanar kasa

Shugaban adawa na Tanzania, Tundu Lissu, ya shaida wa kotu a ranar Litinin cewa an hana shi ‘yancin sa na doka na asali kuma zai kare kansa kan zargin cin amanar kasa wanda ke dauke da hukuncin kisa.

An kama Lissu sau da dama a baya, amma wannan shi ne karo na farko da ya fuskanci irin wannan tuhuma mai tsanani, wanda ya haɗa da yiwuwar hukuncin kisa.

Wannan yana zuwa ne yayin da hukumomi a ƙasar gabashin Afirka ke ƙara matsa lamba kan jam’iyyar adawa ta Lissu, wato Chadema, a gabanin zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokoki a watan Oktoba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button