Labarai
Wani abin fashewa ya kashe mutane uku sannan wasu 21 suka ji raunika a titin Katarko-Goniri da ke ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Akasarin waɗanda suka rasu ƴan garin Gotata ne, kuma motarsu ce ta taka abin fashewar da ake zargi nakiya ce da aka binne, kamar yadda tashar talabijin ta Channels TV ta ruwaito.
A cewar rahoton, garin Gotata na kusa da dajin Sambisa inda mayaƙan Boko Haram suka fake suna kai hare-hare.
A ranar Laraba ma wani bam ya yi ajalin matafiya huɗu a jihar Borno mai maƙwabtaka da Yobe.
Mayaƙan Boko Haram, waɗanda aka fatattaka a baya, sun ci gaba da zafafa kai hare-hare a baya-bayan nan a yankin, lamarin da ya sa ake fargabar ko hanun agogo ya fara komawa baya a yaƙin da ake yi da masu iƙirarin jihadi.



