Dolane shugaban jam’iyar Apc na jihar kano Abdullahi Abbas ya sauka daga shugabncin jihar kano

Kungiyoyin jam’iyyar APC da suka hadar da Kungiyar ƙadangaren bakin tulu da ta yan takwas sun yi kira ga Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas da ya sauka daga kujerar shugabancin jam’iyyar
Shugaban kungiyar yan takwas na jam’iyyar APC Nura Na’annabi da sakataren kungiyar APC Kadangaren Bakin Tulu Kwamared Abubakar Abdullahi Dangarinnan su ne suka bukaci hakan yayin wani taron manema labarai da suka kira a yau dinann,
“A Madadin Kungiyar APC kadangaren Bakin Tulu ta Jihar Kano, Muna yabawa Dr. Abdullahi Umar Ganduje bisa Amsa kiraye kirayenmu da muka dade munayi na cewa ya sauka daga wannan kujera ta Shugaban Jam’iyar APC na Kasa, duba da irin rigingimu da zamansa a wannan kujerar ya haifar,
Muna yaba Masa bisa irin kokarin da yayi na ganin an samu shigowar wasu daga cikin Gwamnoni da Sanatoci da Yan’Majalisar Tarayya dana Jihohi zuwa wannan Jam’iyar,
Hakika abin a yaba masa ne Muna Masa fatan Alheri a duk inda ya tsinci Kansa nan Gaba. ”
Muna so kuma muyi Amfani da wannan dama domin taya sabon Shugaban riko na Jam iyar APC His Excellency Bukar Dalori murnar kama aiki muna Addu’a Allah ya dafa masa.
Sannan muna so muyi Kira gare shi cewa yayi Gaggawar rushe Shugabancin Jam’iyara Matakin Jihohi Musamman na nan Jihar Kano, yin haka zai dawowa da Jam’iyar APC ta Jihar Kano Kwarjinin data rasa tun bayan kasancewar Hon. Abdullahi Abbas a Matsayin Shugaban ta na Jihar Kano”.
Com. Dangarinnan ya ce “Idan kuma Allah yasa shi shugaban Jam’iyyar APC na qasa ya ji kiraye kirayen da muke cewa Lokaci yayi da zaiyi ƙoƙari wajen dinke kowace irin ɓaraka da Shugabancin su Ganduje da Abdullahi Abbas suka haifar mana na rabe-raben kawunan Yan’ Jam’iyyar, musamman a nan Jihar Kano, to hakika Jam’iyyar zata isa inda ake da bukata, Kuma tafiyar zata haifar da ɗa mai ido.




