Aƙalla mutum 38 ne suka rasu, sannan wasu 28 suka jikkata bayan wani hatsarin mota, inda motoci biyu suka ƙone bayan sun yi taho mu gama a arewacin Kilimanjaro a Tanzania.

Kwamishinan yankin Kilimanjaro, Nurdin Babu ya ce hatsarin ya auku ne da yammacin ranar Asabar a lardin Same bayan tayar ɗaya daga cikin motocin ya fashe, suka haɗe, sannan wuta ta tashi.
Mutum 22 daga cikin 28 da suka jikkata sun samu sauƙi har an sallame su daga asibiti, amma akwai guda shida da suke cigaba da jinya.
Shugaban ƙasar Samia Suluhu ta nuna rashin jin daɗinta kan yawaitar hatsari a ƙasar, inda ta ce alƙaluman hatsarin suna ɗaga hankali.
Daga watan Janairu zuwa watan Afrilu, an yi hatsari 1,322 a ƙasar, inda mutum 1,275 suka mutu, wanda ƙari ne a kan irin wa’adin nan a bara da kashi tara.
A ranar 8 ga watan Yuni, mutum 28 suka rasu a babbar hanyar Tanzania-Zambia da ke kudancin yankin Mbeya lokacin da wata babbar motar ɗaukar kaya ta ƙwace, ta buga da ƙananan motoci biyu.




