Ketare

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai sun yi “babban lahani” ga cibiyoyin nukiliyar ƙasar.

A wata tattaunawa da gidan talabijin gwamnati da aka yi da shi da yammacin Alhamis, Araghchi ya ce hukumar kula damMakaman nukiliya ta Iran tana gudanar da cikakken bincike don tantance girman ɓarnar da aka yi.

Sai dai, awanni kaɗan kafin hakan, shugaban addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bayyana cewa hare-haren ba su hana ci gaba da shirin nukiliyan kasar ba.

Ya mayar da martani ne ga iƙirarin Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya ce hare-haren sun “lalata gaba ɗaya” wurare uku na nukiliyar ƙasar.

Khamenei ya ce hare-haren Amurka “ba su cimma wani abu mai muhimmanci ba,” tare da zargin Trump da zuzuta girman tasirin hare-haren.

Ya kuma ayyana cewa Iran ta samu nasara akan Amurka da Isra’ila.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button