Ketare

Larurar zazzagowar al’aura: ‘Na ji kamar wani abu na sauka a farjina’

Helen Ledwick ta zama mai wayar da kan mata bayan fama da larurar gocewar ƙugu

Kusan shekara 10 da suka wuce, lokacin da Helen Ledwick ta rubuta “me ya sa nake jin kamar gaɓoɓina na karairayewa?” a shafin matambayi ba shi ɓata na Google, ba ta taɓa tunanin irin amsar da za ta samu ba.

Tsohuwar ma’aikaciyar BBC ɗin ta gano tana fama da larurar gocewar ƙugu ko kuma pelvic organ prolapse (POP), wadda ke shafar ɗaya cikin mata 10 bayan haihuwa.

Larurar na faruwa ne lokacin da ɗaya ko fiye cikin gaɓoɓin ƙugu, kamar mafitsara ko makasaya kokuma mahaifa, suka matsa daga inda suka saba kuma suka takure bangon farjin mace.

Wannan larura ba ta kisa, amma za ta iya jawo matsala a rayuwar yau da kaullum, da alaƙar auratayya, da ma lafiyar ƙwaƙwalwa.

Cikin alamomin matsalar sun ƙunshi jin nauyi ko kuma jin alamun wani abu na sauka cikin farjinta – wasu kan siffanta jin abin tamkar mace ta “zauna kan ƙwallon tennis”.

A wajen Ledwick, ta gamu da larurar ne bayan mako biyu da haihuwar ɗanta na biyu.

“Kawai na tashi zaune na fara jin komai na motsawa,” a cewarta. “Kamar an matsar da audugar al’ada daga wajenta. Kana ji ka san akwai matsala.”

Bayan ta shiga damuwa, ta ɗauki madubi da kuma wayarta domin tabbatar da abin da ke faruwa.

“Ban taɓa jin kalmar prolapse ba kafin lokacin,” a cewarta. Kuma tun da ta fara magana kan lamarin, ta fahimci abu ne da mutane ba su magana akan sa.

Ledwick na ganin tsangwamar da ake nuna wa masu larurar na taimakawa wajen rashin wayar da kai game da ita a tsakanin mata.

Helen Ledwick ta ce wani likita ne ya gano matsalar tata, abin da ya firgita ta.

“Na zaci za a yi min dogon bayani, a ba ni magani, a fara kula da ni cikin gaggawa. Amma kawai sai aka fara ba ni amsa rabi da rabi.”

An ba ta shawarar ta guji yin ayyukan da za su iya ta’azzara larurar, kamar gudu da tsalle da ɗaga kayan nauyi.

“Sai na ji kamar ana ce min ‘kada ki ci gaba da rayuwarki’,” in ji ta.

“Muna zaune cikin kunya da kaɗaici. Saboda ba mu yin magana a kai, muna jin kamar mu kaɗai ne muke fama da larurar.”

Ledwick ta buɗe asusu a dandalin Instagram na sada zumunta. A nan ne ta hadu da wasu matan – wasu daga ciki na kunyar neman taimako – abin da kuma ya ƙarfafa mata gwiwar fara gabatar da shiri ta intanet da kuma rubuta littafi mai suna “Why Mums Don’t Jump” – “Me Ya Sa Iyaye Ba Za Su Iya Yin Tsalle ba”.

“Raina a ɓace yake saboda babu wanda yake magana kan matsalar. Shi ya sa na fara magana,” kamar yadda ta yi bayani. “Ina son bai wa mata bayanan da za su sha wahala kafin su same su.”

Helen Ledwick ta zama marubuciya domin wayar da kan mata kan laruruwar gocewar ƙugu

Dr. Nighat Arif, likitar mata ce kuma ta ce matsalar Helen ba sabuwa ba ce, sannan kuma ba kodayaushe ake jin alamunta cikin sauƙi ba.

“Wani lokacin babu alamun a bayyane, kawai sai dai a ji matsi a ƙasan baya da gaba da kuma saman kugu,” in ji ta.

“Alamun za su iya ƙaruwa yayin jima’i, abin da mutane ke kunyar magana a kan sa.”

Abubuwa da dama kan haddasa prolapse, kamar ɗaga kayan nauyi, da yin ƙiba mai yawa, da cushewar ciki. Wasu lokutan takan shafi maza amma ƙalilan.

Ɗaukar ciki da kuma haihuwa ta gaba kan ƙara yiwuwar kamuwa da larurar, musamman idan ta zo da doguwar naƙuda.

Ana ganin mata na ƙara shiga haɗarin kamuwa da ita yayin da suke ƙara shekaru har zuwa lokacin da za su daina jinin haila.

Motsa gaɓɓan ƙugu kan taimaka wajen rage yawan matsalar, amma wani zubin sai likita ya taimaka, kamar saka na’ura a cikin farji da za su taimaka wa bangwayenta, ko kuma yin tiyata.

Larurar gocewar ƙugu na faruwa ne idan ɗaya daga cikin ƙasusuwan da ke tallafa wa ƙungun ya ɗan yi raunin da ba zai iya riƙe su ba

Gano larurar da maganinta

A cewar ƙungiyar likitoci mata ta Brazil mai suna Febrasgo, akan gano larurar ne ta hanyar dubawa sosai da ƙwararriyar likitar mata za ta yi. Hakan zai ƙunshi shaƙa da fitar da nimfashi ba tare da buɗe baki da hanci ba.

A cewar Febrasgo, magani ko jinyar prolapse ya danganta da girman matsala ko kuma yawan sauran matsaloli da mace ke da su, kamar cutar ƙoda ko matsalar fitsari.

“Misali, idan sashen da ke kula da mafitsara ya samu matsala, mace za ta ji alamu kamar wahala wajen yin fitsari da kasa fitar da fitsari gaba ɗaya lokaci guda da kuma yawan kamuwa da ƙwayoyin cutar mafitsara,” a cewar Marcelo Lemos dos Reis na ƙungiyar CRM-SC mai lura da masu larurar.

Ƙungiyar Febrasgo ta ce maganin prolapse zai iya zama na aikatawa da hannu ko na likita. Na hannun ya ƙunshi saka na’ura a cikin farjin mace kamar yadda muka yi bayani a sama.

Kafin a yi tiyata sai an nazarci nau’in matsalar, da wurin da ta shafa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button