Ketare

Yadda ƙasashen yamma ke taimakon Rasha a yaƙinta da Ukraine

Har yanzu Rasha na cigaba da samun biliyoyi wajen sayar da makamashinta ga ƙasashen waje, kamar yadda alƙaluma suka nuna, wanda hakan ke taimakon ƙasar wajen samun kuɗaɗen yaƙinta da Ukraine – wanda yanzu ke cikin shekara ta huɗu.

Tun farkon yaƙin a watan Fabrailun 2022 zuwa yanzu, Rasha ta samu kuɗin shiga daga sayar da makamashi da ya kai ninki uku na tallafin da Ukraine ke samu daga ƙawayenta.

Alƙaluman na nuni da cewa ƙawayen Ukraine na yammacin duniya sun ba Rasha kuɗi ta hanyar sayen makamashi sama da tallafin da suka ba Ukraine ɗin.

Masu suka suna ganin akwai buƙatar gwamnatocin turai da arewacin Amurka su ƙara ƙaimi wajen daƙile ɓangaren man fetur da gas domin kawo ƙarshen yaƙin ƙasar a Ukraine.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button