Labarai
Babban Sufetan ‘Yan Sanda na kasa Kayode Adeolu Egbetokun, ya yi umarni a gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da wani tsohon hafsan ƴansanda ya yi cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, dangane da fanshon tsofaffin ƴansanda.

IGP ya umarci hukumar fanshon ƴansanda ta NPF da ta duba ƙorafin cikin gaggawa, ta gano duk wata matsala, tare da ɗaukar matakin da ya dace don magance matsalolin da aka bayyana.
Kakakin rundunar ta ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar 26 ga Yuni, 2025.
A sanarwar, Egbetokun ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi watsi da halin da tsofaffin jami’anta suke ciki ba, musamman duba da irin gudummawar da suka bayar wajen kare rayuka da dukiyar ƴan ƙasa.
Ya ƙara da cewa biyan fansho cikin lokaci na da matuƙar tasiri wajen ƙarfafa gwiwa da mutuncin rundunar.
Ya kuma ce rundunar za ta ci gaba da sauraron ra’ayoyi da ƙorafe-ƙorafe domin inganta tsarin jin daɗin ma’aikata




