‘Mun cimma Bello Turji har gida mun kashe yaransa’

Haɗin gwiwar jami’an sa-kai a jihar Zamfara sun yi wa riƙaƙƙen ɗan fashin dajin nan mai ƙaurin suna, Bello Turji ƙofar rago a wata maɓoyarsa tare da gwabza ƙazamin faɗa.
Hukumomin jihar sun ce jami’an sa-kai sun yi nasarar kashe mayaƙan Bello Turji fiye da 100 a farkon wannan mako.
Sun ƙaddamar da harin ne da gudunmawar wani tubabben ɗan bindiga, Bashari Maniya wanda ya jagoranci kai farmakin a kusa da ƙauyen Cida na ƙaramar hukumar Shinkafi.
Mataimaki na musamman kan harkokin tsaro ga Gwamnan Zamfara, Alhaji Ahmad Manga ya ce “an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya”.
‘Yan sa-kan CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji.
Majiyoyi sun ce an kuma kashe jami’an sa-kai da wani soja sannan da Bashari Maniya.
Wani ɗan jarida mai bibiyar rikicin ‘yan fashin daji a Arewa maso Yamma ya ce daga bayanan da ya samu, an yi wa motarsu Bashir Maniya kwanton ɓauna ne, inda aka kashe shi tare da wasu jami’an JTF uku.
Wannan dai kusan shi ne karon farko a cewar gwamnatin jihar Zamfara, da jami’an tsaron da ta samar suka samu nasarar kai farmakin har maɓoyar babban ɗan fashin daji.
Bello Turji riƙaƙƙen jagoran ‘yan fashin daji ne da ya dade yana addabar sassan jihar Zamfara da sauran maƙwabtan jihohi.
Hukumomin Najeriya sun kwashe tsawon shekaru suna nemansa ruwa a jallo kuma a baya-bayan nan sun daɗa ƙaimi a ƙoƙarin kama shi musamman bayan kashe wasu manyan ‘yan fashin daji irinsa kamar Halilu Sububu da Manore da Damuna.
‘Za mu ci gaba da farautar Bello Turji’
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun na ranar Litinin da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka fara da ɗan fashin dajin tamkar buɗe sabuwar ƙofar ci gaba da yaƙarsa ne.
“Alhamdulillahi an tarar da shi har gida nai inda ba a taɓa zuwa ba, kuma ya ga cewa ana iyawa, kuma an isko shi” in ji Ahmad Manga.
Ya ƙara da cewa “an kuma buga wuta, an yi nasarori da dama inda aka kashi mutanensa, wanda shi kansa bai iya ƙididdige abin da ya rasa, sai dai daga baya”.
Ya ce duk inda ka ga gawawwaki to akasari na yaransa ne.
Mataimaki na musamman kan sha’anin tsaron ya ce Bashari Maniya ya gamu da ajalinsa ne sakamakon hatsarin da motarsu ta yi lokacin da ta faɗa wani rami.
“Sabuwar mota ce wanda ba duk mutum ya san kanta ba, sun taka wani rami ne mai kama da rijiya kuma suna a guje, motar ta ƙwace kuma ta je ta faɗi. Ba wai shi ne ya yi nasarar buge motar ba, a’a.”
Ya ƙara da cewa lokacin da aka kai musu ɗauki an samu Maniya da sauran waɗanda ke cikin motar ne ba a hayyacinsu ba, saboda motar harbi ba ya ratsa ta.
Alhaji Ahmad Manga ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar Zamfara za ta ci gaba da farautar Bello Turji ba rdare ba rana.
“Wallahi sai abin da ya ci gaba. Alhamdulillahi! Duk ɗan jihar Zamfara zai gaya maka musamman ɗan yankin Shinkafi sun sani, abin da aka yi shekara 14 yana gallaza wa mutane. Shi ya san rawar da jami’an tsaro suka taka yanzu ba a taɓa isko shi ba, irin yadda aka tarad da shi har gidansa.
Ya bayyana aniyar gwamnatin Zamfara na shigo da ƙarin dakarun sojoji don ci gaba da tunkarar Bello Turji
A cewarsa, ko a faɗan da aka yi ranar Litinin Bello Turji laɓewa ya riƙa yi, kafin daga bisani ya arce.
Shi dai Mannir Fura Girke, ɗan jarida mai bibiyar rikicin ‘yan fashin daji Mannir Fura Girke ya ce a iya saninsa Bashir Maniya, ‘yan’uwan Kachalla Dull ne wanda su Bello Turji suka kashe a 2022 amma ya tuba tare da ɗan’uwansa Kabiru Maniya inda suke taimaka wa jami’an tsaro.
Ya ce faɗan yaƙi ne na sunƙuru tsakanin jami’an tsaron Najeriya da kuma su kansu ‘yan fashin daji.
Bayanai dai sun tabbatar da cewa an kai harin karkashin jagorancin Bashari Maniya, wanda tsohon dan bindiga ne da ya taba kai hare-hare a yankunan a can baya kafin ya tuba, inda suka aukawa sansanin Bello Turjin har ma ta kai da dama daga mayakansa suka rasa rayukansu.
Wasu rahotanni dai sun ce kafin kai wannan harin, ɗan bindigar Bello Turji ya samu labarin hakan, inda ya tattara mayaƙa da yawansu ya kai dubu daya domin tunkarar jami’an tsaron.




