Ketare
Akalla mutane 16 ne suka mutu, kuma 400 suka jikkata, yayin da aka kama 61 a zanga-zangar da aka gudanar a fadɗin Kenya jiya, domin tunawa da shekara daya da zanga-zangar adawa da ta biyo bayan ƙarin haraji da gwamnatin ƙasar ta yi.

Hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasar (KNCHR) ta tabbatar da mutuwar mutane 8 da harbin bindiga ya kashe a wurare kamar Machakos da Makueni da Kiambu da Nakuru da kuma Nyandarua.
Amma rahoton Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa Amnesty Kenya ta ce mutum 16 ne suka mutu.
An samu hargitsi da tarzoma a wurare da dama, ciki har da toshe hanyoyi da jifa da duwatsu da amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwa zafi da kuma yunkurin mamaye Majalisa dokokin ƙasar.
Hukumar sadarwa dai ta hana yada shirye-shiryen kai tsaye, amma gidajen rediyo da talabijin sun ƙi bin umarnin.



