ALHAKKU HUMAN RIGHTS & SOCIAL JUSTICE ORGANIZATION TA MIKA SAQON TA’AZIYYAR TA GA AL’UMMAR JAHAR KANO DA MA QASA BAKI DAYA.

A tattaunawar Shugaban Qungiyar wato Comrade Saeed Bin Usman da wakilin AHRASJO NEWS Buhari Ali Abdullahi ya bayyana mana Alhinin wannan qungiya da saqon Ta’aziyyar Qungiyar cewa:
“Suna na Saeed Bin Usman, Shugaban Qungiyar Kare hakkin ɗan Adam da fafutukar tabbatar da daidaiton adalci a cikin al’umma, mai suna Alhakku Human Rights & Social Justice Organisation.
A madadi na da sauran ya’yan wannan qungiya na qasa gaba-daya, muna miqa sakon Ta’aziyyar mu ga Jama’ar Jahar Kano da sauran al’ummar duniya baki daki daya.
Tare da rokon Allah S.W.A ya yi Rahma a gare su, ya kankare dukkan kurakuransu.
Allah S.W.A ya baiwa zuri’ar su hakurin rashi, sannan ya yi albarka ga abinda suka bari”
A cewar Comrade Saeed Bin Usman: muna jinjina da yabawa ga gomnatin Jahar Kano bisa karramawa da mutunta tare da fifita rayuwar ɗan Adam akan komai, duba da yadda jahar kanon ta tsayar da komai don jajantawa iyalan al’ummar da abin ya shafa, tare da rokon malamai wajen ci gaba da nema musu rahamar Allah.



