Vietnam ta kawo karshen hukuncin kisa ga laifukan da suka shafi kasa, cin hanci, da miyagun kwayoyi

Vietnam za ta kawo karshen hukuncin kisa ga nau’ikan manyan laifuka guda takwas – ciki har da almundahana, yunkurin kifar da gwamnati da lalata kayayyakin more rayuwar gwamnati, kamar yadda kafafen yada labarai na gwamnati suka ruwaito.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasar Vietnam, mallakar gwamnati, ya bayar da rahoton a ranar Laraba cewa Majalisar Dokokin ƙasar ta amince da gyaran dokar Laifuka da ta soke hukuncin kisa ga laifuka takwas.
Daga wata mai zuwa, mutane ba za su sake fuskantar hukuncin kisa ba saboda cin hanci, almubazzaranci, samar da magunguna na jabu, safarar miyagun kwayoyi ba bisa ka’ida ba, leken asiri, “laifi na lalata zaman lafiya da haifar da yakin basasa”, da kuma zagon kasa da kokarin hambarar da gwamnati.
Hukuncin mafi tsanani ga waɗannan laifukan yanzu zai zama ɗaurin rai da rai, in ji kamfanin dillancin labarai.
Wadanda aka yanke wa hukuncin kisa saboda manyan laifuka kafin ranar 1 ga Yuli, amma ba a aiwatar da hukuncin ba tukuna, za a sauya musu hukuncin zuwa na daurin rai da rai, in ji rahoton.




