Trump ya bayyana cewa wuraren nukiliyar Iran sun ‘lalace gaba ɗaya’ a hare-haren da Amurka takai

Shugaban Amurka Donald Trump ya dage cewa hare-haren da aka kai kan wasu wuraren nukiliyar Iran a makon da ya gabata sun “lalata gaba daya” wuraren, yana musanta rahotannin kafofin watsa labarai na Amurka da ke ambaton kimar Pentagon cewa hare-haren sun jinkirta shirin nukiliyar Tehran ne kawai na ‘yan watanni.
Wani binciken farko na leken asiri ya nuna cewa harin bama-baman Amurka bai yi nasarar lalata wuraren nukiliyar karkashin kasa na Iran ba, kamar yadda The New York Times, The Washington Post da CNN suka ruwaito a ranar Talata, suna ambaton jami’ai da suka san da rahoton leken asirin soja daga Hukumar Leken Asiri ta Tsaron Pentagon.
Trump ya jaddada cewa hare-haren Amurka sun lalata wuraren nukiliya a Fordow, Natanz da Isfahan.
Lokacin da ‘yan jarida suka tambaye shi game da Iran sake gina shirin nukiliyarta a ranar Talata, Trump ya ce: “Wannan wuri yana karkashin dutse. Wannan wuri an rusa shi.”



