Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kakkausar suka tare da yin Allh-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasa biyu ‘yan jihar a garin Makurɗi, babban birnin jihar Benue.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce, a ranar Litinin ne da misalin ƙarfe 11:00 da dare wasu da ba a san ko su waye ba suka far ma matasan biyu – Barhama Suleiman da Jamilu Ahmad, inda suka yi musu kisan-gilla.
A sanarwar gwamnan ya bayyana harin a matsayin na dabbanci da rashin imani da hankali, wanda ba za a lamunta da shi ba.
A yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga ‘yan uwa da iyalan mamatan Abba Kabir ya jajanta wa fitaccen malamin nan na addinin Musulunci Sheikh Ibrahim Khalil wanda shi ne tamkar mahaifi a garesu.
Sannan ya roƙi jama’ar jihar ta Kano da su kwantar da hankalinsu, inda ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya wajaba don ganin an yi bincike a kan lamarin tare da hukunta waɗanda suka yi kisan.




