Labarai

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano Za Ta Fara Hana Mata Zama Gaban Direbobin Adaidaita Sahu

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kammala shirye-shiryen fara aiwatar da dokar hana mata fasinjoji zama a gefen direbobin Adaidaita Sahu, a wani yunkuri na inganta tarbiyya da tsaftace harkar sufuri a cikin al’umma.

Daraktan Wayar da Kai na hukumar, Auwalu Ado Sheshe, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a.

Ya ce za a aiwatar da dokar ne tare da hadin gwiwar kungiyar direbobin Adaidaita Sahu da masu ababen hawa, domin kauce wa ayyukan da ka iya jawo fushin Allah (SWT) da kuma tabbatar da bin ka’idojin addinin Musulunci.

A cewarsa, matakin zai mayar da hankali ne wajen hana mata zama kusa da direbobin da ba su cikin maharamansu yayin tafiya.

Hukumar ta umarci dukkan direbobin Adaidaita Sahu da su kiyaye wannan doka domin guje wa fuskantar hukunci daga hukumomi.

Haka zalika, ta gargadi mata fasinjoji da su guji zama a gaban direbobi domin kare mutuncinsu da na iyalansu.

 

Sanarwar ta kara da cewa hukumar ta shirya tsaf domin aiwatar da matakin, tare da jaddada kudirinta na gina al’umma mai tsafta da tarbiyya bisa koyarwar addinin Musulunci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button