Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga Iran da ta ‘ci gaba da Bada hadin kai’

Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya (IAEA) ya ce yana maraba da sanarwar da aka yi a yau game da halin da ake ciki a Iran.
“Ci gaba da haɗin gwiwa tare da IAEA yana da mahimmanci ga cimma yarjejeniya ta diflomasiyya don warware takaddama kan ayyukan nukiliyar Iran,” in ji Rafael Grossi.
Ya kara da cewa ya rubuta wa ministan harkokin wajen Iran don jaddada muhimmancin yin aiki tare da bayar da shawarar su hadu nan ba da jimawa ba.
Masu binciken IAEA sun kasance a Iran duk tsawon rikicin kuma suna shirye su fara aiki da wuri-wuri, in ji ƙungiyar a cikin wata sanarwa.
A lokacin waɗannan hare-hare, mun ga mummunan lalacewa a wurare da dama na nukiliya a Iran, ciki har da wuraren canza uranium da kuma wuraren ƙara ƙarfin uranium.




