Ketare
Kawancen NATO sun shirya amincewa da karin kasafin kudi mai yawa na tsaro a taron koli na Hague

Amurka tana ƙara matsa lamba ga kawayenta dasu dauki sabbin matakan manufofi na kashe kudi kan tsaro a matsayin martani ga barazanar Rasha.
Shugabannin duniya da dama sun taru a Netherlands don taron shekara-shekara na Kungiyar Tsaro ta Arewa ta Atlantika (NATO), inda ake sa ran mambobin za su amince da karin kudade ga tsaro a matsayin martani ga matsin lamba daga Amurka.
Trump ya nemi kawayen kungiyar NATO da su kara kashe kudi kan tsaro zuwa kashi 5 cikin 100 na tattalin arzikinsu (GDP), daga burin yanzu na kashi 2 cikin 100. Ya tambayi ko ya kamata kawancen ya kare kasashen da suka kasa cimma burin kashe kudin, har ma ya yi barazanar ficewa daga kungiyar.




