Ketare
Hatsarin mota a Peru ya kashe akalla mutane 15

Wata bas da ke tafiya daga Lima zuwa birnin La Merced ta yi hatsari a ranar Juma’a, inda akalla mutane 15 duka mutu yayin da aka Samu jikkatar kusan wasu 30, in ji mahukunta.
Daraktan lafiya Clifor Curipaco daga yankin Junin a Peru, ya ce motar bas din ta bar kan hanya ta fada cikin kwazazzabo a gundumar Palca.
Hukumomi suna cikin aikin gano gawarwaki 15, in ji Aldo Tineo, wani jami’in kiwon lafiya daga tsakiyar birnin Tarma.
Wata babbar motar bas mai hawa biyu mallakar Expreso Molina Líder Internacional tana dauke da fiye da mutane 60 lokacin da ta yi hatsari kuma ta jirkice a kan rufinta kusa da wani kogi.
Gidan talabijin na ƙasar ya watsa bidiyon inda hatsarin ya faru, wanda ke nuna motar bas ta rabu gida biyu.




