Haɗin gwiwar sojojin RSF ya kafa gwamnati mai zaman kanta a Sudan da ke fama da yaƙi

Wani kawancen Sudan da kungiyar sojojin sa kai ta Rapid Support Forces (RSF) ke jagoranta ya sanar da kafa wata gwamnati madadin a matsayin kalubale ga mahukuntan sojoji a babban birnin Khartoum, yayin da yakin basasar kasar dake arewa maso gabashin Afirka ya shiga shekara ta uku.
Rukunin, wanda ke kiran kansa Majalisar Jagoranci ta Kungiyar Kafa Sudan (TASIS), ya ce shugaban RSF Mohamed Hamdan “Hemedti” Dagalo zai jagoranci majalisar shugaban kasa mai mambobi 15 na gwamnati, wanda ya hada da gwamnonin yankuna.
Ɗan siyasar Sudan Mohammed Hassan Osman al-Ta’ishi zai zama firaminista, in ji TASIS.
Sabuwar gwamnatin da ta ayyana kanta na iya zurfafa rarrabuwar kawuna kuma ta haifar da gasa tsakanin hukumomi yayin da yaki ke ci gaba tsakanin RSF da Rundunar Sojojin Sudan (SAF).
A cikin watan Mayu, sojojin Sudan sun ce sun kori RSF gaba ɗaya daga babban birnin, Khartoum.
Fadan ya faro ne tun daga Afrilu 2023 ya kashe dubban mutane kuma ya raba kusan mutane miliyan 13 daga muhallansu, a cewar kiyasin Majalisar Dinkin Duniya.




