Ketare
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bukaci China da ta dakatar da Iran daga rufe mashigar Hormuz, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga sufurin man fetur na duniya.

Rubio ya yi wannan kira ne bayan rahotanni daga gidan talabijin na gwamnati a Iran sun bayyana cewa majalisar dokokin ƙasar ta amince da wani shiri na rufe mashigar, kodayake hukuncin ƙarshe yana hannun majalisar tsaron ƙasa ta Iran.
Ya ce rufe mashigiar zai yi wa tattalin arzikin ƙasashe wanda zai fi shafar China, wacce ke sayen mafi yawan man fetur daga Iran,kuma suna da alaƙa me ƙarfi da Tehran.
Ya kuma gargaɗi cewa hakan zai shafi tattalin arziƙin sauran ƙasashe fiye da na Amurka.
Kusan kashi 20 na man da duniya ke amfani da shi na wucewa ta mashigin Hormuz, kuma duk wani yunkuri na dakile harkokin sufuri a nan na iya janyo tashin farashin mai a duniya.




