Me dokar hana yaɗuwar makaman nukiliya ta ƙunsa?

Iran ta sake yin barazanar ficewa daga yarjejeniyar taƙaita yaɗuwar makaman nukiliya, yayin da ake tsaka da yaƙi tsakaninta da Isra’ila.
A ranar 13 ga watan Yuni ne Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin soji da ƙwararrun masana nukiliyar Iran da wsu wuraren da ake zargi na da alaƙa da shirin nukiliyar Iran.
Gwamnatin Isra’ila ta ce ta ƙaddamar da hare-haren ne domin hana Iran ƙera makamin nukiliya, tare da kawar da abin da ta kira barazana ga tsaronta.
Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran gudanar da zagayen gaba na tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran a ƙasar Oman, inda jami’an Iran da na Amurka za su tattauna da nufin dakatar da ƙasar daga shirinta na nukiliya.
A nata ɓangare Iran ta ci gaba da jaddada cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya, tana mai cewa ba ta da aniyar ƙera makamin nukiliya.
Haka kuma Hukumar Kula da Makaman Nukiliya ta Duniya, (IAEA) ta bayar da rahoton cewa babu wata hujja da ke nuna cewa Iran ta mallaki makamin.
To amma hukumar ta sha gargaɗin cewa Iran din ta ƙara inganta sinadaran uranium da ya kusa kai wa matakin ƙera nukiliya, wani abu da ya haifar wa ƙasashen duniya fargaba.
Shin mece ce yarjeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya? Mene ne maƙasudinta, Waɗannen ƙasashe ne suƙa ki shiga yarjejeniyar?
1- Yaushe aka ƙirƙiri yarjejeniyar kuma me ya sa?
An buɗe yarjejeniyar don sanya mata hannu a shekarar 1968, kuma ta fara aiki a 1970.
An bayyana yarjejeniyar a matsayin tushe a zamanin hana bazuwar makaman nukiliya.
Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Kula da Makaman Nukiliya ta Duniya ne suka jagoranci yarjejeniyar.
Bayanan yarjejeniyar sun buƙaci ƙasashen da suka amince da ita su biyayya ga buƙatar Majalisar Dinkin duniya na hana bazuwar makaman nukiliya.
An gina yarjejeniyar kan imanin da aka yi cewa yaƙin nukiliya zai haifar da mummunar ɓarna ga ɗan’adam, don haka rage yaɗuwar makaman zai taimaka wajen rage zaman tankiya a duniya, tare da inganta aminci tsakanin ƙasashe.
Ƙunshin yarjejeniyar ya buƙaci dakatar da ƙera makaman, da kawar da waɗanda ake da su, da kuma toshe hanyoyin samar da su, domin kawar da duk wata fargaba ta tayar da duniya da makaman.
2- Muhimman tanade-tanaden yarjejeniyar
Yarjejeniyar mai saɗara 11 ta ƙunshi yadda za a tafiyar da waɗanda ake da su da musayarsu da kuma ƙera makaman, sannan kuma ta ƙarfafa gwiwar masu shirin amfani da makamashin nukiliya don zaman lafiya.
Muhimman tanade-tanaden yarjejeniyar su ƙunshi:
Ƙasashen da suka mallakai makamin kada su yarda su bai wa wata ƙasa makamin, sannan ka da ta yarda ta bai wa wata ƙasa damar iko da makamanta, sannan kada su taimaka wa ƙasar da ba ta da makamin wajen mallakarsa ke ƙera shi.
Su kuma ƙasashen da ba su da makamin, kada su ƙera ko su mallaka ko su karɓa daga wata ƙasar, sannan kada su nemi taimakon fasaha a wannan fanni.
Haka kuma an buƙaci ƙasashen da ba su da makamin, kuma suke da buƙatar makamashin don zaman lafiya, su sanya hannu kan yarjejeniyar kariya da hukumar IAEA don tabbatar da cewa ba a karkatar da sinadaran uranium da fasahar wajen ƙera makamin ba. Kuma hukumar IAEA za ta riƙa sanya idanu don tabbatar da ɗorewar hakan.
Babu wasu kayan haɗa sinadaran, ko fasahar ko kayan aikin haɗa makamin da aka yarje a kai wata ƙasar da ba ta da nukiliya, in ba wadda ta sanya hannu kan yarjejeniyar kariya da IAEA ba.
Yarjejeniyar ta kuma tanadi “cikakken yanci” ga duka ƙasashen da ke cikin jarjejeniyar da su inganta tare da amfani da makamashin nukiliya don dalilan zaman lafiya ba tare da nuna bambanci ba.
Yarjejeniyar ta kuma bai wa ƙasashen da ke cikinta ‘yancin ficewa daga yarjejeniyar, idan suka yi amanna cewa wani yanayi na cutar da muradinsu, kuma dole su bayar da sanarwar ficewar a hukumance wata uku kafin ficewar ga ƙasashen da ke cikin yarjejeniyar da kuma Kwamitin Tsaro na Majalisar dinkin Duniya, tare da bayyana dalilansu na ficewar.
3- Waɗanne ƙasashe ne suka sanya hannu a yarjejeniyar?
Mafi yawan ƙasashen duniya sun shiga cikin Yarjejeniyar Takaita Yaɗuwa Makaman Nukiliya tun bayan ɓullo da ita a 1968. A shekarar 1995 aka faɗaɗa ta ta yadda aka bar ta a buɗe na har abada.
Yanzu haka akwai ƙasashen duniya 191 da ke cikin yarjejeniyar, lamarin da ya sa ta kasance yarjejeniyar duniya da ƙasashe suka fi sanya hannu a kanta.
Biyar daga cikin ƙasashen na da makaman nukiliya, yayin da sauran suka ƙudiri aniyar kada su mallaka ke ƙerawa ko karɓa daga wata ƙasa.
4- Ƙasashen da suka mallaki makamin a cikin yarjejeniyar?
Ƙasashe biyar da yarjejeniyar ta bayayna da ”masu makamin nukiliya” su ne: Amurka da Rasha da Birtaniya da Faransa da kuma China.
An lissafa waɗannan ƙasashe ne saboda ko sun taɓa gwajin makamin kafin ranar 1 ga watan Janairun1967, abin da ya sa yarjejeniyar ta bayyana su da kasancewa su kaɗai suka mallaki makamin.
Haka kuma ƙasashe su ne masu kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
To sai dai duk da sanya hannu kan yarjejeniyar da waɗannan ƙasashe suka yi, ƙasashe marasa nukiliya sun riƙa sukarsu kan abin da suka bayyana da tsantsar nuna wariya.
Babu wani ƙayyadajjen wa’adi da aka sanya na lalata nukiliyar waɗannan manyan ƙasashe, wanda ke nuna bambanci tsakanin ƙasashe tare da yin barazana ga tsarin daidaito tsakanin ƙasashe.
Hakan ya sa wasu ƙasashen suka yi imanin cewa dokokin da aka sanya wa ƙasashe mara makaman sun fi tsauri, fiye da waɗanda aka sanya wa ƙasashen da suka mallaki makamin, lamarin da ya sa wasu ke ganin anya jarjejeniyar da gaske take wajen lalata makaman ake da su?
5- Waɗanne ƙasashe ne ba sa cikin yarjejeniyar?
Akwai ƙasashe huɗu da har yanzu ba su shiga cikin yarjejeniyar ba, waɗanda suka haɗ`a da:
– Isra’ila
– India
– Pakistan
– Koriya ta Arewa
Da farko Koriya ta arewa ta shiga yarjejeniyar a 1985, to amma 2023 ta bayyana ficewarta, inda a baya-bayan nan take yawan gwajin makaman nukiliyar.
Isra’ila ba ta tabbatar da mallakar makamin a hukumance ba, amma ana yi mata kallon wadda ta mallake shi.
Waɗannan al’amura na ƙara tayar da tambayoyi game da ikon da yarjejeniyar ke da shi na tilastawa ƙasashe shiga cikinta, ganin yadda waɗannan ƙasashe masu ƙarfin tasirin soji da siyasa suka ƙi shiga cikinta.




