Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na yaki da kwararowar hamada da inganta yanayi ta hanyar dashen itatuwa

Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Dakta Dahir M. Hashim, ya jaddada kudurin a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Talata.
Dokta Hashim ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki a ’Yan Bawa da ke karamar Hukumar Makoda, wadda ke dauke da daya daga cikin manyan wuraren rainon itatuwa a Najeriya.
A cewarsa, sama da shuka 75,000 ne ake rainon su a yankin a wani bangare na shirin dashen itatuwa miliyan biyar na gwamnati na shekarar 2025.
Ya jaddada cewa kwararowar hamada da fari na haifar da babbar barazana ga dan adam da kuma dabbobi, yana mai jaddada cewa aikin fadada matsugunin ya kasance wani muhimmin bangare na dabarun jihar na kare kai daga gurbacewar kasa.



