Kwamitin Majalisar Dattawa yana shiri kan Sauya Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999
Kwamitin wanda ke ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin, ya shirya wani taron jin ra’ayoyin jama’a na kwanaki biyu a yankuna shida na ƙasar don tattara ra’ayoyin ’yan Najeriya game da sabbin gyaran da ake shirin yi a kundin tsarin mulki.
Sanarwar batutuwan da za’a tattauna sun hada ‘yancin kan ƙananan hukumomi, gyaran harkokin zaɓe da na shari’a, kirkiro sabbin jihohi, kafa ‘yan sandan jihohi da yadda da yan takarar Independent,da bawa yan Nigeria na kasashen waje damar yin zabe.
Za a gudanar da taron na shiyyar Kudu maso Yamma a jihar Lagos, saina shiyyar Arewa maso yamma a Kano dana Kudu maso Gabas a Enugu, da Jos a shiyyar Tsakiyar kasar,sai Maiduguri a Arewa maso Gabas, daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Yuli, 2025.
Za a Tattauna kudururruka Sama da 20 da Suka Shafi Tsaro, Tattalin Arziki da sauransu.




