Ketare

Trump ya “ci amanar” Iran da jama’ar Amurka kan hare-hare data kai – Ministan Harkokin Wajen Iran

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya mayar da martani ta gidan talabijin kan hare-haren da aka kai wa wuraren nukiliyar kasarsa, inda yake cewa Trump ya “yaudari” duka Iran da mutanen Amurka.

Sakataren wajen Burtaniya yace Ba a yi amfani da sansanin sojan Biritaniya da ke Diego Garcia ta jiragen saman sojan Amurka don gudanar da hare-haren bama-baman su kan Iran ba.

Saidai yace Amurka ta gudanar da hare-haren bama-bamai daga tsibirin da ke cikin Tekun Indiya a baya, amma ba ta yi hakan ba a wannan karon.

Tun da farko, sakataren harkokin wajen Birtaniya ya tabbatar da cewa ba ta shiga cikin hare-haren da Amurka ta kai kan wuraren nukiliyar Iran ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button