Ketare
Yan Najeriya mazauna kasar Israila na neman agajin Gwamnatin Tarayya kan su kai musu dauki bayan barkewar yaki a kasar.

Cikin wani rahoto da Jaridar Punch ta wallafa, ’yan Najeriyar sun zargi gwamnati da rashin kai masu ɗauki yadda ya kamata, inda suka ce tuni sauran ƙasashe suka fara kwashe ’yan ƙasarsu.
Rahoton ya bayyana cewa ’yan Najeriyar sun fi yawa a birnin Ƙudus da Tel Aviv, inda Iran ta tsananta kai hare-hare.
A halin yanzu sun bayyana cewa suna ɓoye ne a wurare da babu tabbas kuma rayuwarsu na cikin haɗari, a koyaushe komai na iya faruwa da su.




