Labarai

Sojojin Runduna ta 6 sun lalata wuraren tace haramtaccen mai da dama a yankin Neja Delta, musamman a Jihar Ribas, tare da kama mutane 50 da ake zargi.

A yayin aikin daga 30 ga Yuni zuwa 13 ga watan Yuli, 2025, sojojin sun ƙwato sama da lita 25,000 na man da aka sace da kuma gano hanyoyin da ake amfani da su wajen satar mai daga bututun gwamnati.

An kuma kama wasu mutane a Jihar Delta, Bayelsa da Akwa Ibom, inda aka gano kwale-kwale da jarkoki ɗauke da haramtattun man fetur.

Sojoji sun ce za su ci gaba da kare dukiyoyin mai na ƙasa da kuma hana ayyukan laifi a yankin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button