DA DUMI-DUMI: Jigawa za ta samar da kashi 25 na shinkafar da Nijeriya ke bukata, cewar Hon. Abdurrahman Salim Lawan Gwaram

Shugaban karamar hukumar Gwaram kuma sabon shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi Nijeriya reshin Jihar Jigawa, Hon Abdurahman Salim Lawan Gwaram ya bayyana cewa Jigawa za ta samar da kashi 25 na shinkafar da Nijeriya ke bukata
Hon Abdurahman Salim Lawan Gwaram, ya ce Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Nnamdi Danmodi ya yi tsari ta yadda nan da dan lokaci kadan da ikon Allah Jigawa za ta noma shikafa kashi 25 cikin 100 na shinkafar da Nijeriya take bukata a duk shekara.
Ya kara da cewa Gwamna Danmodi ya yi tsari na samar da tan 300 wanda kowanne mazabar dan majalisar jiha za ta samu tan goma, sai kuma kari da za a bai wa hamshakan manoma kari kan 300 na mazabu kananan hukumomin Jihar 27, ga shirin tallafawa manyan manoma 1,000 da za su noma hekta 500 a Jihar ta Jigawa, akwai tsarin tallafa wa manoma 200 a kowacce karamar hukuma ta jihar ta hanyar ba su kayan aikin noma.




