Labarai

An kashe wasu matafiya ɗaurin aure a garin Mangu na jihar Filato

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na daren jiya Juma’a, kuma yanzu haka 11 daga cikin matafiya na kwance a asibiti.

Jaridar ta ruwaito cewar mutanen na kan hanyar zuwa ƙaramar hukumar Qua’an Pan, lokacin da wasu ɓatagari suka farmusu.

Ibrahim Umar, ɗaya daga cikin waɗanda suka kuɓuta, ya ce suna kan hanyar zuwa ɗaurin ne suka ɓace hanya, don haka suka tsaya don yin tambaya, amma sai dai kuma ɓatagari suka farmusu da muggan makamai, inda suka fara da kashe direba sannan sauran mutane, kafin daga bisani su cinnawa motar da gawarwakin wuta.

A wata sanarwa da ƙungiyar al’ummar Musulmi ta ƙaramar hukumar Mangu ta fitar, wacce ta samu sa hannun shugabanta ta Sheikh Suleiman Haruna ta yi alawadai da lamarin, inda ta buƙaci gwamnati ta tabbatar da an kamo waɗanda suka aikata laifin, don a hukuntasu.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar ta Filato DSP Alfred Altau, ya ce sun samu labarin faruwar lamarin, kuma da zarar sun kammala tattara bayarai za su fitar da sanarwa a kai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button