Ketare

Wanne bom ne mai ƙarfi na Amurka zai iya lalata rumbunan nukiliyar Iran?

Jirgin Amurka mai suna US B-2 ne kawai zai iya ɗauka tare da harba bom ɗin GBU-57A/B da zai iya ketawa har ya kai wurin rumbunan ajiyar sinadaran nukiliyar Iran

Daga cikin makaman da za a iya harbawa su keta ƙarƙashin ƙasa har su iso wurin da rumbunan ajiyar sinadaran nukiliyar Iran suke, daya ne kawai ba a yi amfani da shi ba zuwa yanzu, kuma Isra’ila ba ta da shi a yanzu.

Makamin shi ne GBU-57A/B – wanda ya kasance bom marar nukiliya mafi ƙarfi a duniya – da zai iya lalata rumbunan ajiyar sinadaran ƙera makamin nukiliya, kuma Amurka ce kadai ta mallake shi a duniya.

Wannan tsararren makami mai nauyin kilogiram 13,600 zai iya ketawa ƙarƙashin ƙasa domin wargaza rumbunan sinadaran ƙera nukiliyar Iran da ke binne can ƙarƙashin duwatsu.

Zuwa yanzu Amurka ba ta bai wa Isra’ila makamain ba.

To amma shi wannan makami ya yake, mene ne kuma ƙalubalen amfani da shi?

Gwamnatin Amurka ta ce bom ɗin GBU-57A/B wani ”babban makami ne mai ƙarfin da zai iya ketawa ƙarƙashin ƙasa ya y tafiya mai nisa domin wargaza rumbunan da hanyaoyin da aka gina can ƙarƙashin ƙas.

Makamin mai tsawon mita shida, an yi amanna cewa zai iya tafiyar ƙafa 200 (mita 61) a cikin ƙasa kafin ya fashe. Za kuma a iya jefa wasu boma-boman su bi shi yayin da za su iya nutsewa fiye da inda ya tsaya.

Bom ɗin na MOP – da kamfanin Boeing ta ƙera shi – ba a taɓa amfani da shi ba a tarihi, to amma an taɓa yin gwajinsa a cibiyar gwajin makaman Amurka ta ‘White Sands Missile Range’ da ke jihar New Mexico.

Bom ɗin MOP ya zarta na MOAB, mai nauyin kilogiram 9,800, da ake yi wa laƙabi da ”uwar boma-bomai”, wanda aka yi amfani da shi a yaƙin Afghanistan.

”Daga nan ne rundunar sojin Amurka ta ƙudiri aniyar ƙera wasu takwarorinsa masu irin girmansa, ko ma waɗanda za su zarta shi ɓarna. Lamarin da ya sa suka samar da GBU-57A/B mai keta ƙarƙashin ƙasa,” a cewar Farfesa Paul Rogers, na cibiyar nazarin zaman lafiya a Jami’ar Bradford da ke Birtaniya UK.

Haka kuma kawo yanzu jirgin Amurka mai suna US B-2 Spirit – da ake wi wa lakabi da sha kundum – ne kawai zai iya ɗauka tare da harba bom ɗin na MOP.

Kamfanin ƙera makamai na Northrop Grumman ne ya ƙera jirginm kuma ya kasance ɗaya daga cikin jiragen yaƙin Amurka na zamani.

Kamfanin da ya ƙera jirgin ya ce, B-2 zai iya ɗaukar nauyin da ya kai kilogiram 18,000.

Rundunar sojin saman Amurka ta ce ta yi nasarar yin gwajin jirgin ɗauke da boma-boman GBU-57A/B har guda biyu, wadanda nauyinsu ya kai kilogiram 27,200.

Wannan jirgi zai iya yin tafiyar kilomita 11,000 ba tare da buƙatar sake shan mai ba, kuma zai iya tafiyar kilomita 18,500 da shan mai ɗaya, lamarin da zai ba shi damar isa kowane wur a duniya cikin sa’o’i, a cewar kamfanin da ya ƙera jirgin.

Farfesa Rogers ya ce idan za a a harba bom din MOP kan ƙasa da ke da ƙarfin tsaron sararin samaniyarta, kamar Iran, jirgin B-2 zai saje ne cikin wasu jiragen yaƙin domin ɓad da kama.

Alal misali za a iya amfani da jirgin F-22 domin gigita tsaron maƙiya, sannan kuma da jirage marasa matuƙa domin gano irin ɓarnar da aka yi, don gano ko akwai buƙatar ƙarin hare-hae domin ruguza cibiyoyin tsaron samaniyar.

Farfesan ya yi ƙiyasin cewa Amurka ba da wadatattun irin waɗannan boma-boman.

“Wataƙila irinsa da suke da shi bai wuce 10 zuwa 20 ba,” in ji shi.

An yi amanna cewa makamin zai iya keta ƙarƙashin ƙasa ya yi nisan ƙafa 200, kafin ya fashe.

Za a iya amfani da bom ɗin MOP kan Iran?

Fordo ce cibiyar nukiliyar Iran ta biyu mafi girma bayan Natanz, wadda ke kan gaba.

An gina ta ne a yanki mai duwatsu kusa da birnin Qom, kusan kilomita 95 kudu maso yammacin birnin Tehran.

An yi amanna cewa an far gina cibiyar a wajejen 2006, kuma cibiyar ta fara aiki a 2009, a lokacin da Iran ta bayyana wa duniya wanzuwarta.

Baya ga kasancewarta a ƙarƙashin ƙasa da duwatsu na tsawon mita 80 (ƙafa 260), rahotonni na cewa Fordo na samun kariya daga na’urororin kakkaɓo makamai masu linzami na Iran da Rasha.

A watan Maris din 2023, Hukumar Kula da Makamin Nukiliya ta Duniya, IAEA ta gano sinadarin uranium da ka inganta zuwa kashi 83.7 cikin 100 na matakin ƙera nukiliya a cibiyar.

Firaministan Ira’ila Benjamin Netanyahu maƙasudin kai wa Iran hari shi ne wargaza shirinta na samar da maamin nukiliya, wanda ya bayyana da ”mummunar barazana ga Isra’ila.”

Jami’an sun ce wargaza cibiyar Fordo na daga cikin manufofin

“Wannan gagarumin aiki, za a kammala shi ne da wargaza cibiyar Fordo,” kamar yadda jakadan Isra’ila a Amurka, Yechiel Leiter ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Fox News ranar Juma’a.

To amma Isra’ila ba ta da bom ɗin MOP da zai iya wannan aiki, kuma Amurka ba za ta ba ta damar amfani da shi ba, ba tare da hannun sojojinta ba, kamar yadda Farfesa Rogers ya bayyana.

“Ba za su yarda Isra’ila ta yi amfani da shi da kanta ba, kuma Isra’ila ba ta da jirgin da zai iya dauar bom ɗin.”

Don haka bai wa Isra’ila bom ɗin ya dogara ne da yadda Amurka ta so shiga yaƙin, musamman ƙarƙashin mulkin Donald Trump.

Farfesa Roger ya ƙar da cewa ”ya dogara ne da matakin da Trump zai ɗauka kan shigar Amurka yaƙin”.

An dai tambaye shi a taron G7 ko Amurka za ta shiga yaƙin?, sai ya amsa da cewa ”bana son yin magana game da haka”.

Iran dai ta sha cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne, kuma ba ta taɓa yin tunanin ƙera makamin nukiliya ba.

Amma amkon da ya gabata hukumar kula da nukiliya ta IAEA ya bayayna cewa Iran ta karya dokar haramta yaɗuwar makaman nukiliya karon farko cikin shekara 20.

‘Ba lallai bom ɗin ya iya aikin ba’

Duk da hare-haren baya-bayan nan da Isra’ila ta ƙaddamar kan cibiyoyn nukiliyar Iran, Farfesa Rogers ya ce ya yi imanin cewa ”da wuya Isra’ila ta iya cimma burinta na lalata cibiyoyin nukiliyar Iran da ke binne a ƙarƙashin ƙasa”.

“Dole su buƙaci wani abu kamar bom ɗin MOP domin cimma, abin da ba za su iya cimmawa da kansu ba”.

Shi kuwa Kelsey Davenport, Daraktan cibiyar kula da bazuwar makamai ta Amurka ya ce ”matuƙar cibiyar Fordo na ci gaba da aiki, to akwai hatsarin Iran ta kusa ƙera nukiliya. Iran na da zaɓin ci gaba da inganta sinadarin nukiliya da zai kai matakin ƙera makamin nukiliya a wurin, ko kuma ta sauya wa sinadarn wuri zuwa wani waje”.

Haka kuma ko da an yi amfani da bom din MOP, ba lallai a samu nasarar wargaza cibiyar ba, saboda rashin sanin haƙiƙin tsawon zurfinta da kuma irin kariyar da cibiyar ke da shi, kamar yadda Farfesa Rogers ya yi ƙarin haske.

“A yanzu wannan bom ɗin ne kaɗai aka yi imanin zai iya lalata cibiyoyn nukiyar Iran din da ke can ƙarƙashin ƙasa. To amma zai iya yin hakan ko ba zai iya ba, shi ne har yanzu ba a sani ba”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button