Kungiyar IPOB ta bayyana shari’ar da ake yi wa shugabanta, Nnamdi Kanu da kuma abin da ya faru a gaban kotu a matsayin wani cikakken abin tuhuma kan tsarin shari’ar Najeriya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, mai magana da yawun kungiyar, Emma Powerful, ya ce abin da ya faru a babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Alhamis, ya fallasa yunkurin gwamnatin tarayya na karshe na zargin Kanu a kan zanga-zangar #EndSARS ta 2020.
Powerful ya ce lokaci ya yi da duniya za ta dauki matakin gaggawa kan “karyar” da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi wa shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra a gaban mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ya nanata cewa shari’ar wata makarkashiya ce da aka gina ta kan karya da kuma amfani da kafafen yada labarai.
Powerful ya ce daga cikin abubuwan da suka tada hankali a kotun har da cewa babu wata shaida ta jami’an tsaro 200 da ake zargin an kashe a yankin Kudu maso Gabas, inda ya ce ba a gabatar da suna, babu mukami, babu tashoshi da kuma takardar shaidar mutuwa da aka gabatar.




