Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da soke dukkanin tsarin kananan makarantun sakandare na (JSS) da manyan makarantun sakandare na (SSS) a kasar nan.
Gwamnatin ta gabatar da sabon tsarin karatun bai daya na shekaru 12, wanda zai bai wa yara damar neman ilimin firamare da sakandare a hade.
Kafin daukar wannan mataki ana kan tsarin 6-3-3-4 wato shekaru 6 a Furamare da shekaru 3 a karamar sakandire da shekaru 3 a babbar sakandire sai kuma shekaru 4 a makarantar gaba da sakandire.
Rahotanni nacewa, gwamnatin tarayyar ta koma kan tsarin 12 da kuma 4 wato an hadewa dalibai neman Ilimi daga Furamare har sakandire.
Haka kuma, an nemi majalisar koli kan ilimi ta kasa ta amince da shekaru 16 a matsayin mafi ƙanƙantar shekarun shiga jami’o’i a kasar nan.




