Isra’ila na cigaba da harin ta’addanci Wanda ya kashe Falasdinawa masu fama da yunwa yayin da jakadan Amurka ya ziyarci wuraren agaji

Aƙalla mutane biyu sun mutu kuma fiye da 70 sun jikkata yayin da suke jiran kayan abinci a kusa da Morag Corridor kudu da Khan Younis a safiyar Juma’a, in ji wakilin Al Jazeera Arabic.
Jakadan Amurka Steve Witkoff da jakadan Amurka a Isra’ila, Mike Huckabee, sun ziyarci wuraren rarraba agaji a Gaza yayin da mace-mace daga yunwa ke ci gaba da karuwa a yankin Falasdinawa.
Likitoci a Gaza sun ba da rahoton cewa wasu jarirai biyu da wani saurayi sun mutu saboda yunwa a karkashin takunkumin da Isra’ila ta kakaba kan tallafin jin kai.
Yawan mutanen da suka mutu saboda yunwa a Gaza yanzu ya kai 154, ciki har da yara 89.
Yakin Isra’ila a Gaza ya kashe akalla mutane 60,249 kuma ya jikkata wasu 147,089.
An kiyasta cewa mutane 1,139 ne aka kashe a Isra’ila yayin harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba, 2023, kuma fiye da 200 aka kama su.



