Ketare

An yanke wa mutane biyu hukuncin daurin shekaru 30 kan harin otal din Kenya na 2019

Wata kotu a Kenya ta yanke wa wasu maza biyu hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari saboda taimaka wa mayakan al-Shabab da suka kai wani mummunan hari a Nairobi wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 21 a shekarar 2019.

A ranar Alhamis, Alkalin kotu Diana Kavedza Mochache ta yanke hukunci cewa Hussein Mohammed Abdile da Mohamed Abdi Ali sun taka muhimmiyar rawa ta hanyar taimaka wa wasu biyu daga cikin masu harin su tsere daga sansanin ‘yan gudun hijira ta amfani da katunan shaida na bogi. Su biyun kuma sun bayar da taimakon kudi ga kungiyar.

An sanar da hukuncin Abdile da Ali a watan da ya gabata saboda taimakawa da kuma hada baki don aikata wani aikin “ta’addanci”. Dukkan mutanen biyu sun musanta zarge-zargen kuma yanzu suna da kwanaki 14 don daukaka kara.

Kungiyar Al-Shabab mai dauke da makamai mai alaka da al-Qaeda ta dauki alhakin kai harin, inda ta ce harin na ramuwar gayya ne ga matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button